Matsalolin girgizar kasa da igiyan ruwa na Tsunami sun janyo cikas wa aiyukan tashar nukiyar kasar Japan. Wannan ya janyo mahukuntan kasar da sauran kasashe tashi tsaye domin magance matsalolin.
Sauran kashi-kashi
-
A duk shekara Nijar na asarar Eka ko kadadar noma dubu dari sakamakon zaizayewar Ƙasa
‘Muhallinka Rayuwarka’ shiri ne da zai leka Jamhuriyar Nijar, inda wani rahoton ma’aikatar kididdiga ke cewa a duk shekara kasar na asarar Eka ko kadadar noma dubu dari sakamakon zaizayewar Ƙasa da gusowar hamada. Lamarin da ya zama babban koma baya ga ayyukan wadata kasa abinci. Wata matsalar ita ce ta sallacewar kasa da komawarta hako da ba a iya noma a kai.01/06/202420:00 -
Nigeria daya daga cikin kasashe masu noman auguda a nahiyar Afrika da duniya
Shirin a wannan mako zai ba da hankali ne akan noman auduga,a shekarun baya, Nigeria ta kasance daya daga cikin kasashe masu tinkaho da noman auguda a nahiyar Afrika da duniya baki daya.Sai dai hankalin mahukuntan kasar ya koma ga bangaren man petur bayanda Allah ya albarkaci kasar da mai.Jihohin da suka yi fice a noman auduga a kasar, sun hada da Zamfara, Katsina, Kano, Adamawa, Bauchi da kuma Gombe.26/05/202417:54 -
Matsalar yoyon iskar gas yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha yankin Delta
Shirin na wannan mako zai yi dubi ne akan yadda al'ummar karamar hukumar Obagi na jihar RIVERS dake yankin NIGER DELTA tarayyar Najeriya suke fama da matsalar yoyon iskar gas sanadiyar fashewar bututun da aka samu tun a watan Yunin shekarar 2023 wanda yayi sanadiyyar gurbacewar ruwan sha, wanda ya sa al'ummar ke kamuwa da cutar amai da gudawa har zuwa wannan lokaci.04/05/202419:32 -
Matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka don magance matsalar tsuntsaye a gonaki
Shirin 'Muhalli' na wannan makon tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali ne kan tu’annatin da wasu nau'in tsuntsaye da ake kira jan-baki ke yi wa gonaki a Najeriya tare da kokarin da gwamnati ke yi domin shawo kan lamarin.20/04/202419:27 -
Najeriya ta kasance kan gaba a fagen noman masara a yankin yammacin Afrika
Shirin wannan mako zai ba da hankali ne a kan yadda Najeriya ta kasance akan gaba a fagen noman masara a daukacin yankin yammacin Afrika, inda kasar ke samar da sama da kashi 48 na masarar da ake nomawa a yankin.Mafi yawan masarar da ake nomawa a kasar, na fitowa ne daga yankin arewacin kasar, musamman jihohin Bauchi, Kaduna, Borno, Naija da Taraba da kuma wasu ‘yan kalilan din jihohin kudu maso yammacin kasar.23/03/202421:02