Isa ga babban shafi
Togo

Faransa Ta Yafewa Kasar Togo Bashi Kudade

Kasar Faransa ta yafe dimbin bashin da take bin kasar Togo, daya kai kudin Turai Euro Miliyan 100, a wani al’amari da ake ganin anyi ne domin taimakawa kasar ta gyagije daga matsalar komadan tattalin arziki.Jiya ne Jakadun kasashen biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yafe dimbin basukan.Kasar Faransa ta kuma nuna shirin ta na kara taimakawa kasar Togo wajen samun alfarman yafe wasu basukan masu yawan gaske.Hukumomin kasar Faransa na nuna cewa yafe basukan na biyo bayan namijin kokarin da aka ga kasar Togo, mai yawan mutane miliyan 6 da dubu dari 6, tayi ne wajen rage fatara da tada komadan tattalin arzikin ta. 

Shugaban Kasar Togo Faure Gnassingbé
Shugaban Kasar Togo Faure Gnassingbé rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.