Isa ga babban shafi
Siriya

Jamian Tsaron Syria Sun Kashe Mutane 63

A Kasar Syria mutane akalla 63 suka rasa rayukansu lokacin da Dakarun Gwamnati suka bude wuta kan masu zanga zangan lumana don nuna kyamar Gwamnatin kasar.Bayanai na nuna cewa mutane 48 aka kashe a garin Hama inda mutane sama da 500,000 suka taru don nuna kyamar Gwamnatin kasar.A gunduman Homs , inda kamar yankin Hama dake Arewacin Damascus an kashe wasu mutanen, yayin da a yankin Rastan an sami rasa rayuka biyu.Jagoran Kare Hakkin Dan Adan dake kulada kasar Rami Abdel Rahman ya gaskata shaida kisan. 

Masu zanga-zanga na kasar Syria
Masu zanga-zanga na kasar Syria RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.