Isa ga babban shafi
Libya-Japan-NATO

Japan ta kwace kaddarorin Gaddafi

Kasar Japan ta kwace wasu kaddarori na Shugaban kasar Libya Moammar Gaddafi da mukarrabansa, da suka kai na kudin Amirka Dollar samada Billiyan 4.Kaddarorin  sun hada da ajiya a Bankuna kamar dai yadda bayanan ke nunawa.Wani kudirin Majalisar Dinkin Duniya daya sami amincewar  kasashen Larabawa da na kasashen Africa na ranar 26 ga watan biyu na wannan shekaran, ya gindaya takunkumi kan Gwamnatin Moammar Gaddafi saboda yadda ake uzurawa jama'a dake boren lumana don nuna kyamar Gwamnatin kasar.Ya zuwa wayewar gari yau Asabar Dakarun NATO/OTAN na ta kai munanan hare-hare kasar ta Libya domin kawar da Shugaba Moammar Gaddafi daya ki sauka daga mulkin kasar bayan ya kwase shekaru samada 40. 

Bayan harin da aka kai birnin Tripoli sda safe hayaki ya turnuke sararin samaniya
Bayan harin da aka kai birnin Tripoli sda safe hayaki ya turnuke sararin samaniya RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.