Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Boko Haram ta ci gaba da kawo tashin Hankali a Najeriya

Al'amuran yau da kullum, sun tsaya cik jiya a garin Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno dake yankin Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya, sakamakon wani bincike da rundunar dake aikin samar da tsaro suka kaddamar.Ana gudanar da binciken domin gano wadanda suke kai hare hare da bama bamai a garin, mai fama da tashin hankali, da kuma hare hare, wadanda ake zargin kungiyar Jama’atu ahlili Sunnah lidda’awati wal Jihad, da akewa lakabi da Boko Haram da kaiwa.Kungiyar ta ci gaba da kawo barazanar tsaro cikin yankunan arewacin kasar ta Najeriya tun bayan boren da 'ya 'yan kungiyar suka fara tayarwa cikin shekara ta 2009, abun da ya janyo gwamnati ta yi amfani da karfi wajen murkushe shugabannin kungiyar.Kungiyar ta Boko Haram ta dauki alhakin kai hari da bam helkwatar rindinar 'yan sandan kasar cikin watan jiya na Yuni.

Reuters / Afolabi Sotunde
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.