Janhuriyar Demokaradiyar Congo
Jirgin sama ya fadi da Mutane 112 a kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo
Jirgin sama dauke da fasinjoji 112 ya rikito, a filin saukan jiragen saman garin Kisangani na kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo. Kamar jama’ai suka tabbatar.Rahotanni da ba a tantance ba, sun bayyana zakulo mutane kusan 40 da rai.Jirgin ya fadi yayin da yake shirin sauka, lokacin da yanayin sararin samaniya birnin ke dagule, kamar yadda wani jami’in kamfanin jirgi na Hewa Bora wanda ya fadin ya tabbatar.Tuni majjiyoyin gwamnati dake Kinshasa babban birnin kasar ta Janhuriyar Demokaradiyar Congo, suka tabbatar da hadarin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: