Isa ga babban shafi
France-Brazil

Babu Laifin Matukan Jirgin Da Ya Fadi Na Air France

Kamfanin Jiragen Sama na France Air ya karyata cewa ya dora laifin faduwan jirgin sa a shekara ta 2009 akan matuka jirgin, bayan gabatar da wani rahoto yau Jumaa dake nuna cewa matukan sunyi wasu kura-kurai.Wata sanarwa daga kamfanin Jiragen Sama na cewa babu wasu dalilai da zasu sa a zargi matuka jirgin da laifi.Sanarwan na cewa akwai wasu naurori da suka ki aiki, saboda haka ba laifin matukin jirgi bane.Hukumar Jiragen Sama na kasar Faransa, BEA ya dora laifin faduwan jirgin saman fasinjan kan rashin samun cikakken horo na wasu naurorin jiragen sama.Jirgin aman da ake zance ya fada teku ne bayan ya tashi daga Rio-Dejanairo na kasar Brazil zashi Paris, inda mutane 228 suka mutu. 

Nauran nadan magana na jirgin Sama da ya fadi 2009
Nauran nadan magana na jirgin Sama da ya fadi 2009 RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.