Isa ga babban shafi
Palasdinu

Shugaban Palestinu Na New York Don Taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban Kungiyar Palestinawa Mahmud Abbas, ya bukaci kasar Israela da ta amince da kasar Palestinu, don kaucewa wannan daman samun zaman lafiya a yankin.Shugaba Abbas yayi wannan kalamin ne yau lokacin da ya sauka a filin jiragen Sama na New York, don halartan taron Majalisar Dinkin Duniya.Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Hamas ke cewa ba zata goyi bayan gabatar da kudirin ba.Nasirudeen Mohammed ya hada mana rahoto akai. 

Shugaban Palastinu Mahmoud Abbas
Shugaban Palastinu Mahmoud Abbas RFI
Talla

00:57

Nasirudeen Mohammed

A halin da ake ciki Prime Ministan Britaniya, Tony Blair, ya ce dole sai an koma teburin shawara tsakanin Isra’ila da Palasdinu, kafin a cimma wata yarjejeniyar da zatayi tasiri kan bukatunsu.

Yayin da yake maida martani kan shirin gabatar da kudirin kasar Palasdinu a zauren Majalisar Dinkin Duniya, Blair dake cikin masu sasanta bangarorin biyu, ya bayyana cewar.
 

00:10

Tony Blair

"ni abinda nake fadi shine, duk abinda ya faru a Majalisar Dinkin Duniya, dole mu sake komawa teburin shawara, dan fara tattaunawa, domin idan ba muyi haka, ba za’a iya warware matsalar batun iyaka, Birnin Kudus, da Palasdinawa Yan gudun hijira ba."

Yanzu haka dai Shugabannin  Addinin Kirista a Birnin Kudus, sun bayyana goyan bayansu ga shirin kungiyar Palasdinu na samun wakilci a Majalisar Dinkin Duniya.

Wata sanarwa da shugabanin Darikar Catholica, Anglican, Lutheran da kuma Orthodox suka bayar, sun bayyana goyan bayansu kan samun kasar Palasdinu akan iyakokin tan a 1967.

To ko wannan yunkuri na iya samun nasara, tambayar kenan da muka yiwa Dr ElHarun Muhammad, na Babbar kwalejin Fasaha ta Kaduna.

03:39

Dr El-Harun Muhammad

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.