Isa ga babban shafi
Faransa

Yan takara Shugabancin Faransa na jam'iyyar Gurguzu na neman goyon baya

Yan Takaran shugabancin kasar Fransa, karkashin Jam’iyar Gurguzu ta Socialists, Francois Holande, da Martin Aubry, jiya sun sake fafatawa a mahawarar talabijin, dan nemna goyan baya kafin zaben raba gardamar da za’a gudanar a karshen wannan mako.Aubry ta zargi Hollande, da cewar bai taba rike wani babban mukami ba, ko da minista ne, da zai bashi damar kwarewar mulki, yayin da Hollande ya ce shi fatar sa, shine hada kan 'yan Jam’iya domin kauda Shugaba Nicolas Sarkozy daga mulkin, ganin yadda ya batawa kasar suna. Babu dan takara guda da ya samu yawan kuri'un da ya ke bukata, domin takarar Shugabancin kasar ta Faransa wa jam'iyyar gurguzu, yayin zagaye na farko, abunda ya janyo tafiya zagabe na biyu domin tantance gwani.

François Hollande da Martine Aubry, 'yan takarar neman kujerar shugaban kasa karkashin Jam'iyyar Gurguzu
François Hollande da Martine Aubry, 'yan takarar neman kujerar shugaban kasa karkashin Jam'iyyar Gurguzu PATRICK KOVARIK / AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.