Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya bukaci Netanyahu ya bi tafarkin diflomasiya akan Iran

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande, ya bukaci Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da ya goyi bayan bin tafarkin diplomasiya dan warware rikicin kasar Iran, maimakon kaiwa kasar hari. Kasashen duniya na zargin kasar Iran sarrafa Uraniyom domin kera makamin Nukuliya.  

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande REUTERS/Philippe Laurenson
Talla

Hollande ya bayyana haka ne a tattaunawar da sukayi da Netanyahu ta waya, inda ya jadadda bukatar sa na ganin Iran tayi watsi da shirin ta na nukiliya, amma kuma shi baya goyan bayan amfani da karfi.

A makon da ya gabata, Firaministan Isra’ila ya bukaci daukar kwararan matakai kan kasar ta Iran.

A kuma ranar Talatan da ta gabata ne, Netanyahu, ya nuna cewa ba zai ta jiran kasashen duniya da su ke ce mai ya dakata kamin ya dauki wani matakin kai hari kan Iran ba.

Shugabannin biyu dai sun yi alkawarin aiki tare da juna.

Wata sanarwa da Ma’aikatar kasar Amurka ta fitar, ya nuna cewa babu rashin jituwa a tsakanin kasashe akan yadda ake so a tunkari Iran, sai dai sanarwar ta nuna alamun bacin ran shugaba Obama akan kalaman Netanyahu, wanda ya zo dai di lokacin da ake shirin zaben Amurka.

Wata jaridar kasar Birtaniya ta rawaito cewa shugaban hukumar leken asiri ta M16 ya ziyarci kasar Isra’ila domin ya mata gargadi akan kada ta kai hari kan kasar ta Iran.

Kasashen Rasha da Sin da Amurka da Birtaniya da kuma Faransa a karshen taron da aka yi na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya, IAEA, sun soki kasar Iran akan shirin nata.

Kasar Isra’ila dai ce kadai ke da makamin Nukiliya a yankin gabas ta Tsakiya, inda ta ke ganin barin Iran ta mallaki Nukiliyan kan iya zama barazana ga kasarta.

Amurka da Kasashen yammacin duniya suma suna zargin Iran da kokarin kera makamin na Nukiliya, zargin da Iran ta dade tana musantawa, inda ta ke cewa za ta yi amfani da shi ne domin samar da wutar lantarki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.