Isa ga babban shafi
Afghanistan

Afghanistan za ta nemi sasantawa da ‘Yan kungiyar Taliban

Ministan Harkokin Wajen Kasar Afghanistan, Zalmai Rassoul, ya dauki alwashin ganin cewa an sasanta da kungiya Taliban domin kawo karshen tashe tashen hankula da ke faruwa a kasar. Rassoul, ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da wani kwamitin da zai kula da dangantakar kasar ta Afghanistan da kasar Amurka, inda ya ce za su yi kokarisu su ga cewa an sasanta.  

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai
Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Sakartariyar harkokin wajen kasar Amurka, Hillary Clinton, ita ma ta yi alwashin marawa kasar ta Afghanistan baya, ta yadda za ta shawo kan matsalolin kasar, koda dakarun Amurka da NATO sun fice daga kasar.

Taron kaddamar da kwamitin ya kuma tattauna akan matakan da za a dauka na ganin cewa an samar da damar kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Har ila yau taron yazo a dai dai lokacin da rahotanni ke nuna cewa, Amurka na wani shirin ganin cewa an tattauna a kasar ta Afghanistan domin kawo karshen rikice rikicen da ke addabar kasar.

Wasu jami’an soji da diplomasiyar kasashen biyu, sun gayawa mujallar New York Times a wata hira cewa, tattaunawar za a barta ne a hanun gwamnatin Afghanistan, sai dai sun nuna kokwantasu, inda suka ce basa ganin yiwuwar tattaunawar nan kusa, inda su kara da cewa, watakila sai nan da shekara ta 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.