Thomas Lubanga ya daukaka kara kan hukuncin kotun duniya
Mutumin farko da kotun hukunta manyan laifufuka ta ICC ta samu da laifufukan yaki, a Janhuriyar Demokradiyar Congo, Thomas Lubanga, ya daukaka kara kan hukuncin daurin shekaru 14 da aka masa.
Wallafawa ranar:
An dai samu tsohon shugaban 'Yan Tawayen ne da hannu wajen sanya kananan yara yaki wanda ya kaiga kashe mutane 60,000 a shekarar 1999.
Tun dai shekarar 2006 da ake tsare da Lubanga a birnin Haque.
A watan Yulin da ya gabata ne aka yankewa Lubanga, dan shekaru 51, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 14, domin rawar daya taka wajen aikata laifukan yaki.
Rahotanni na nuna cewa akalla mutane sama 60,000 suka mutu a rikicin kasar tun daga shekarar 1999.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu