Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta fitar da tsare-tsaren yin garanbawul ga bankunan kasar

Kasar Faransa ta fitar da jaddawalin tsare-tsaren yin garan- bawul ga bankunan kasar wanda zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin Faransa. Ministan kudin kasar ta Faransa, Pierre Moscovici, dai ya ce a wata mai zuwa ne zai mika tsare-tsaren ga bangaren zartarwa, inda ya kara da cewa, yin hakan zai tantance ayyukan da bankuna ke yi wanda zai taimakawa tattalin arzikin kasar, daga wanda bankunan kan yi dan gashin kansu.  

Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Shugaban kasar Faransa, François Hollande
Talla

Ya kara da cewa, za a tilastawa bankuna su kirkiro da wasu sassa wanda zasu dinga gudanar da hadahadarsu wanda hakan zai sa a samu saukin sakawa bankunan kasar ido.

Wannan tsari dai, a cewar Ministan zai bawa bankuna damar bankuna su shirya yadda zasu kawo karshen hada hadar kasuwancin da bai cimma ruwa ba.

Har ila yau, Ministan kudin ya kara da cewa, tsarin ya hada da sashin noma inda za a saka ido akan kayyayakin da aka fi nema, wanda wasu sukan yi amfani da wannan dama su sa kayyayakin abinci su yi tsada.

Har izuwa lokacin hada wannan rahoto dai, bankunan kasar ta Faransa basu ce komai ba akan wannan tsari da ma’aikatar da kudi zata sa a aiwatar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.