Isa ga babban shafi
Saliyo

An kammala yakin neman zaben shugaban kasa a Saliyo

Yayin da ake shirin gudanar da babban zaben kasar Saliyo a karshen mako, ya zuwa yanzu ‘Yan takarar sun kammala yakin neman zaben. Dubun dubatar magoya bayan ‘Yan takara ne suka yi dandazo a birnin Freetown, inda suka kalli yadda gwanayen nasu suka karkare yakin neman zaben.  

Taswirar kasar Saliyo
Taswirar kasar Saliyo www.jeuneafrique.com
Talla

Zaben na ranar Asabar shine na uku, tun bayan yakin basasan da aka shafe shekaru 11 ana gwabza wa, da kuma ya lakume ran mutane da dama.
 

Magoyaa bayan tsohon shugaban mulkin soja, Julius Maada Bio, kuma babban abokin adawan shugaba mai ci, Ernest Koroma, sun taru a babban filin wasa na birnin Freetown, inda ya yi musu jawabi.
 

A zaben shekarar 2007, jama’iyyar SLPP ta Julius Bio, ta yi zargin an tafka magudi, amma yanzu tsohon shugaban ya ce, ba za su lamunci aringizon kuri’a ba.
 

Ita ma jama’iyyar APC, ta shugaba Koroma, ta kammala nata yakin neman zaben.

Kuma wani na hannun daman shugaban, ya ce suna fatan samun nasara da kashi 65 cikin 100, da za su kaucewa zuwa zagaye na 2.
 

Yayin da ake tunanin shugaba Koroma zai lashe zaben, shi ma Bio na da nashi magoya bayan, lamarin da zai sa a iya zuwa zaben zagaye na 2.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.