Isa ga babban shafi
G8-Birtaniya-Amurka

Taron G8 ya dauki muhimman matakai kan matsalolin da duniya ke fuskanta

Shugabannin kasashe takwas masu karfin tattalin arziki a duniya wato G8, da ke kammala taronsu a kasar Birtaniya, sun mayar da hankali kan batutuwa da dama, musamman ma tattalin arziki, siyasa da kuma sha’anin tsaro a duniya.

Shugabannin G8 a taronsu na Arewacin Ireland
Shugabannin G8 a taronsu na Arewacin Ireland Reuters/路透社
Talla

A game da batun tattalin arziki dai, kasashen sun fi mayar da hankali ne a game da yadda za a hana sulalewar haraji wanda ke kawo wa tattalin arzikinsu matsaloli da dama, yayin da taron G8, ya kuma dauki matakin haramta biyan kudaden fansa ga ‘yan ta’adda domin biya masu da bukatunsu.

To sai dai wani muhimmin batu da taron ya kasa cimma matsaya a kai shi ne rikicin kasar Syria, sakamakon yadda Rasha da ke marawa shugaba Bashar Assad baya ta ki amince da wasu shawarwarin da sauran kasashe a karkashin jagorancin Amurka suka gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.