Isa ga babban shafi
Brazil

An ci gaba da gudanar da tarzoma duk da sassaucin gwamnatin Brazil

Duk da cewa hukumomin kasar Brazil sun sanar da janye karin da suka yi a kudaden sufuri domin kawo karshen zanga zangar gama gari da ke neman durkusar da kasar, amma yunkurin bai samu amincewar masu zanga zangar ba.

Masu zanga-zangar adawa da wasannin gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya da ake gudanarwa a Brazil
Masu zanga-zangar adawa da wasannin gasar cin kofin zakarun Nahiyoyin duniya da ake gudanarwa a Brazil REUTERS/Ueslei Marcelino
Talla

Rahotanni sun ce, masu zanga zangar sun tare hanyoyin motar garuruwan Sao Paulo, Brazilia da Rio de Janaeiro, bayan da hukumomin suka sanar da janye karin.

Wannan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da gasar neman daukar Kofin Zakarun Nahiyoyin Duniya na kwallon kafa, a kasar wadda ke shirin daukar babbar gasar cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya a shekara mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.