Isa ga babban shafi
Amurka-Iran-Isra'ila

Isra’ila na ci gaba da kushewa aikin sarrafa Nukiliyar kasar Iran

Firaiministan kasar Isra’ila Benyamin Netenyahu, ya gargadi shugaban kasar Amurka Barack Obama da kada ya kuskura ya amince da kulla yarjejeniyar da za ta bai wa kasar Iran damar ci gaba da mallakar fasahar Nukiliya

REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Benyamin Netenyahu wanda ke ganawa da shugaba Obama a karon farko tun bayan lokacin da suka samu sabani dangane da batun cijewar tattaunawa tsakanin bangarori biyu kan yadda za’a tinkari rikicin kasar Isra’ila da Palasdinu, ya ce zai zama babban kuskure amincewa Iran ta mallaki fasahar Nukilya.

Firaministan na Isra’ila ya ce Iran na kokarin ganin ta cimma yarjejeniya da manyan kasashen duniya, domin cire mata Takunkummai da kuma kasancewa mai damar sarrafa makamashin Nukiliya, kuma Obama na daga cikin masu kokarin ganin hakan ta faru.

Saboda haka Netenyahu ya bayyana cewa yana fatar ganin hakan ba ta faru ba lokacin mulkin Obama, domin Iran na neman yaudarar Duniya ne a cewar sa.

A cikin makon gobe ne dai ake kyautata zaton cewa Iran da kuma manyan kasashen Duniya 6 za su cimma matsaya kan wannan batu, bayan share kusan watanni 8 suna tattaunawar sulhu a tsakaninsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.