Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya tattauna ne game da dakile dandalaye sadarwa na Twitter da YouTube a kasar Turkiya, shin ko ya wannan matakin ya shafi masu mu’amula da dandalayen musamman ma dalibai. Shirin ya ji ta bakin wasu dalibai ‘Yan Afrika da ke karatu a Turkiya.
Sauran kashi-kashi
-
Yadda Dalibai ke bada gudunmawa wajen sarrafa sinadaran da basa gurbata muhalli
Shirin ilimi hasken rayuwa na wannan mako ya duba yadda Dalibai a kasashen da suka ci gaba ke bayar da gudunmawa wajen sarrafa sinadarin "Hydrogene" da baya gurbata muhalli sosai, ta fuska kere-kere da nufin inganta iskar da ake shaka, bisa tallafin gwamnatocin kasashensu.14/05/202410:01 -
Taro kan gudummawar kafafen yada labarai a bangaren tsaro a jami'ar ABU Zaria
Matsalar tsaro na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, musamman ma arewacin kasar, hakan ya sanya sashen koyon aikin jarida na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da ke jihar Kaduna ya shirya wani taro gagarumin taro na kasa da kasa domin tattaunawa a kan gudumawar da kafafen yada labarai za su iya bayarwa wajen warware matsalar tsaro. Ya yi wannan ne da zummar taimaka wa kokarin da al'umma ke yi wajen warware wa kansu matsalar tsaron da ke damun su.05/03/202409:57 -
Yadda amfani da komfuta ya shafi kyaun rubutun dalibai
A wannan makon zamu duba yadda ci gaban kimiyya da Ilimi ke zama wani nau’I na koma baya musamman a tsakanin dalibai a Najeriya.Tun bayan samar ko kuma kirkirar na’urar kwamfuta a 1837, da kuma shigowar ta Najeriya karon farko a 1963 sannu a hankali take bazuwa tsakanin jama’a, yayi da kuma ake samun ci gaba ta fannin amfani da ita.31/01/202409:34 -
Gwamnatin Neja na shirin farfado da tsarin karatun makiyaya
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon zai yi duba ne da tsarin karatun 'yayan makiyaya, wato Nomadic Education. Gwamnatin jihar Neja ce ta yi hobbasa don farfado da shirin karatun 'yayan makiyaya a jihar. Shirin zai bai wa makiyaya damar samun ilimi a duk inda suka yi balaguro don inganta makomarsu. Yanzu haka dai shirye-shirye sun yyi nisa a game dfdaa wannan shirin a jihar Neja mai fara da matsalar tsaro sakamakon ayyukan 'yan bindiga da ke kashe mutane da satar su don kudin fansa.19/12/202309:56 -
Iyayen dalibai a Nijar na kokawa kan tsadar kudin karatu
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Shamsiyya Haruna ya maida hankali ne kan yadda iyaye ke kokawa a jamhuriyar Nijar kan tsadar kudin karatun 'ya'yansu, masamman makaruntu masu zaman kansu saboda matsaloli na tsadar rayuwa da aka shiga tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki.14/11/202310:08