Isa ga babban shafi
Tarin Fuka

Masu fama da tarin fuka sun ragu a duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, ta gano cewa an samu saukin yawan mutanen da ke kamuwa da cutar tarin fuka a bara, idan aka kwatanta da shekarar 2019 da mutane miliyan 1 da dubu dari hudu suka kamu.

Kimanin mutane miliyan 1 da dubu 500 ke mutuwa a kowacce shekara saboda cutar tarin fuka.
Kimanin mutane miliyan 1 da dubu 500 ke mutuwa a kowacce shekara saboda cutar tarin fuka. AFP/File
Talla

WHO ta ce ta gudanar da binciken ne a kasashe sama da 80, inda aka samu ragi da kaso 21 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2019.

Kasashen Indonesia da Afrika ta Kudu da Philiphines da India na cikin kasashen da ke kan gaba wajen raguwar mutanen da ke kamuwa da cutar.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce bullar annobar Corona ma ta dakile yakin da ake yi da tarin fukar, kasancewar da fari an sanya ran ragin ya fi haka.

Tedros ya kuma ce akwai bukatar kasashen duniya su sake zage damtse wajen yaki da tarin fukar don kauce wa kashe kudin maganinta babu gaira babu dalili.

Ya ce, wayar da kan mutane a game da illar cutar, da kuma gaggawar zuwa asibiti da zarar an ji alamun ta za su taka rawa ainun wajen magance cutar cikin hanzari.

A cewar sa WHO ba za ta tsagaita a yakin da ta ke yi da tarin fukar ba, har sai ta tabbatar cewa an kai cutar kasa, amma samuwar hakan sai da hadin kan kasashe a cewarsa.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.