Isa ga babban shafi
WHO-Unicef

Miliyoyin kananan yara na fuskantar barazana saboda rashin rigakafi

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da asusun UNICEF da kuma hadakar Gavi sun yi gargadi kan yadda rayukan miliyoyin yara ke cikin hadari sanadiyyar muggan cutukan da ke musu barazana saboda gazawa wajen yi musu alluran rigakafin da suka kamata.

Kananan yara fiye da miliyan 200 ne suka rasa rigakafi saboda yadda Duniya ta mayarda hankali wajen yaki da Covid-19.
Kananan yara fiye da miliyan 200 ne suka rasa rigakafi saboda yadda Duniya ta mayarda hankali wajen yaki da Covid-19. REUTERS/Olivia Acland
Talla

Hukumomin Lafiyan na WHO da UNICEF da kuma Gavi cikin sanarwar hadakarsu kan makon rigakafi da aka fara yau Litinin, sun bukaci daukar matakan gaggawa wajen yiwa yaran rigakafin da ya kamata da nufin ceto su daga barazanar da ke tunkararsu.

Sanarwar ta ruwaito shugaban WHO Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus na cewa hadin kan duniya wajen tunkarar matsalar ne kadai zai ceto kananan yaran daga halaka sakamakon tsanantar cutuka irinsu kyanda da hangun da kuma shawara.

Wani binciken hukumar WHO kamar yadda sanarwar ta bayyana ya nuna cewa duk da nasarar da aka samu a yaki da Covid-19 fiye da kashi 1 bisa ukun kasashen Duniya 37 cikin dari na fuskantar koma baya a rigakafin kananan yara.

Sanarawar ta ce fiye da kasashe 50 ne suka dakatar da rigakafin gama gari yayinda kananan yara miliyan 228 suka rasa damar karbar rigakafin cutuka masu alaka da shawara da Polio da kuma kyanda.

A kokarin tunkarar matsalolin karkashin bukukuwan makon rigakafin, hukumar WHO da Gavi da kuma UNICEF sun kaddamar da wani gagarumin shiri mai taken Immunization Agenda 2030 da ke da nufin karfafa tsarin rigakafi da kuma hana yankewar alluran a a kowanne yanayi.   

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.