Isa ga babban shafi
Corona-G20

Kananun kasashe za su samu allurai biliyan 3 da rabi daga manyan kamfanoni

Manyan Kamfanonin samar da maganin rigakafin cutar corona na duniya na Pfizer da Moderna da Johnson and Johnson sun shaidawa taron kungiyar kasashe masu arziki na G20 cewar za su taimakawa kasashe matalauta da allurar rigakafi biliyan 3 da rabi a farashi mai sauki a cikin wannan shekara da shekara mai zuwa.

Hadakar kamfanonin 3 sun raba adadin da kowanne cikinsu zai samarwa matalautan kasashen.
Hadakar kamfanonin 3 sun raba adadin da kowanne cikinsu zai samarwa matalautan kasashen. FRANCOIS LO PRESTI AFP/File
Talla

Wakilan kamfanonin sun shaidawa taron dake gudana yau cewar Pfizer zai samar da alurar biliyan 2, Moderna zai samar da miliyan 995 sai kuma Johnson and Johnson da zai samar da allura miliyan 500.

Wannan na daga cikin gudumawar da kamfanonin za su bayar wajen ganin wadannan kasashe sun yi nasarar yiwa jama’ar su allurar rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.