Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinu

Isra'ila ta yi musayar rigakafin Korona da Falasdinu

Isra’ila za ta bai wa Falasdinu kimanin alluran rigakafin Covid-19 miliyan guda a karkashi wata yarjejeniyar musayar rigakafin.

Allurar rigakafin Korona
Allurar rigakafin Korona REUTERS - LUCY NICHOLSON
Talla

Ofishin Firaministan Isra’ila ya fitar da wata sanarwa da ke cewa, kasar ta sanya hannu kan wata yarjejeniya domin bai wa Falasidnu rigakafin Korona na Pfizer kimanin miliyan guda da ke gab da cimma wa’adinsu na lalacewa.

A karkashin wannan yarjejeniya ta musaya, Isra’ilar za ta karbi wasu alluaran na daban daga kamfanin Pfizer da suka kamata a aika wa Falasdinawa tun da farko.

Nan da watan Satumba mai zuwa ne, ake sa ran kamfanin na Pfizer ya biya Isra’ila kwatankwacin adadin alluran da ta bai wa Falasdinu.

Kamfanin na Pfizer ne dai ya jagoranci wannan yarjejeniya domin gaggauta shirin yi wa al’umomin bangarorin biyu rigakafin cutar.

An cimma yarjejeniyar ce bayan Isra’ila ta yi  la’akari cewa, a yanzu ba ta da bukatar alluran rigakafin kuma tuni aka fara mika dubu 100 na alluran ga Falasdinu.

Ya zuwa yanzu, Isra’ila ta yi wa kashi 55 na al’ummarta  rigakafin Korona a zangon farko da na biyu, wato adadin da ya yi daidai da miliyan 5 da dubu 100, yayin da a jumulce, Falasdinu ta yi wa jama’arta dubu 270 kacal rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.