Shirin Amurka na tallafawa kasashen Duniya da alluran rigakafin Korona
Amurka ta ce ta raba allurai sama da milyan dari daya ga kasashen duniya don yi wa jama’a rigakafin kariya daga cutar covid-19.Amurka ta ce an bayar da wadannan allurai ne ga kasashe akalla 60, mafi yawa karkashin shirin Covax, sai kuma wasu kasashen Afirka da na yankin Carrebean.
Wallafawa ranar:
A Afrika,kasashe irin su Najeriya da Nijar na daga cikin wandada suka amfana da wannan tsari duk da jan kaffa da ake ci gaba da samu a wadanan kasashe na cewa jama' a na ci gaba da dar-dar wajen karbar wannan allura.
Ko a makon da ya gabata Ministan kiwon lafiyar Jamhuriyar Nijar Dokta Illiassou idi Mainassara ya bayyana tsarin da hukumomin na Nijar suka bullo da shi wajen fadakar da jama'a don ganin sun yi na'am da wannan allura.
Tsarin da hukumomin kasashen keda shi,yiwa kusan kashi 30 na jama'ar kasar nan da watan Nuwamba na shekarar bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu