Isa ga babban shafi
WHO-Coronavirus

WHO ta sahale fara yiwa jama'a allurar rigakafin covid-19 sau 3

Kwararrun hukumar Lafiya ta Duniya WHO kan sha’anin rigakafi sun amincewa mutane da ke da garkuwa jiki mai rauni su karbi rigakafin covid-19 fiye da sau 2 na dukkanin nau’ikan alluran da ake amfani da su a yanzu.

Rigakafin Covid-19 samfurin kamfanin Moderna.
Rigakafin Covid-19 samfurin kamfanin Moderna. JOEL SAGET AFP
Talla

Acewar kwararrun na WHO, mutane da shekarunsu ya haura 60 kuma suka karbi alluran rigakafin cutar samfurin Sinovac da Sinopharm na China suna da bukatar karin allura guda don samun cikakkiyar kariya daga cutar.

WHO da ke tsokaci kan matakin bayan tun farko Amurka ta shiga sahun farko wajen baiwa al'ummarta rigakafin a karo na 3 sabanin 2 da hukumar ta sahale, ta ce mutane da dama na bukatar karin allurar rigakafin a karo na 3 don samun cikakkiyar kariya daga cutar.

Kudirin Majalisar Dinkin Duniya na ganin ta yiwa kashi 10 na al’ummar kowacce kasa rigakafin cutar kafin karshen watan Satumban da ya gabata ya gamu da cikasa saboda karancin alluran rigakafin a kasashe 56 ko da ya ke kasha 90 na manyan kasashe sun cimma kudirin.

Hukumar ta WHO ta koka da yadda har yanzu kaso mai yaw ana kasashen Duniya ke fama da kamfar allurar duk da fatan da ake da shin a ganin fiye da kasha 2 bisa 3 na al’ummar Duniya sun karbi rigakafin kafin karshen shekara.

Acewar hukumar ta na duba yiwuwar bayar da damar yiwa mutane allurar a karo na 3 la’akari da karancin alluran a wasau kasashe musamman na matalauta.

Sashen kwararrun kan sha’anin rigakafi a hukumar wanda ake kira da SAGE zai sake nazarin batun tare da fitar da matsaya a ranar 11 ga watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.