Isa ga babban shafi
Coronavirus-WHO

Sabon nau'in Korona na da mugun hadari - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa sabon nau’in cutar Covid-19 da ya bulla na Omicron na da matukar hadari a duk duniya baki daya, duk da cewa har yanzu babu cikakken bayani game da saurin yaduwarsa, idan an kwatanta da na baya.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus,
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, © Laurent Gillieron/Keystone via AP
Talla

Hukumar Lafiyar ta ce sabon nau’in da aka gano a Afrika ta Kudu na da matukar hadari yayin da take nuna alamun saurin kisan wadanda ta kama, baya ga raunana garkuwar jikin wanda ta kama ta yadda magungunan da ake bayarwa zai yi wuya su yi tasiri.

WHO din ta ce abin fargaba ne yadda cutar ke nuna alamun mamaye kasashen duniya cikin hanzari a don haka ya zama wajibi kasashe su mayar da hankali wajen daukar matakan hana yaduwarta cikin gaggawa.

Duk da cewa har yanzu babu rahoton mutuwa sandiyyar kamuwa da nau’in na Omicron, sai dai kuma akwai fargabar samun mace-macen la’akari da hadarinta.

Hukumar lafiyar ta duniya ta ce ya kamata bullar wannan nau’in na Korona ya sanya kasashe su kara azama wajen yi wa jama’arsu rigakafin.

Ya zuwa yanzu dai sabon nau’in cutar da ya fara bulla a Afrika ta Kudu ya bulla a kasashen Birtaniya da Indonesia da Kuwait da Netherlands da Qatar da Saudi Arabia sai Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.