Kasashen G7 sun kadu da sabon nau'in Korona
Gungun kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 ya bayyana fargabar game da barazanar sabon nau’in cutar Korona na Omicron da ya bulla a Afrika ta Kudu, yayin da Bankin Raya Kasashen Afrika ya dakatar da taron da ya shirya gudanarwa a birnin Abidjan saboda bullar cutar.
Wallafawa ranar:
Fargabar ta G7 na zuwa ne bayan da cutar ta yadu a kusan kasashe 7 na duniya, yayin da wasu suka fara janye alaka da Afrika ta Kudu da kuma hana jama’arsu ziyartar kasar.
A cewar kasashen, a yanzu duniya na cikin fargabar fuskantar barazanar cutar mai tsanani, wanda kuma hakan ke bukatar daukar mataki cikin gaggawa a cewar Ministocin Lafiyar kasashen.
Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana cutar a matsayin mai matukar hadari wadda kuma ke barazanar mamaye dukkanin kasashen duniya cikin hanzari.
Watakila wannan fargaba ce ta sanya Bankin Raya Kasashen Afrika dakatar da taron da ya shirya gudanarwa na shekara-shekara a birnin Abidjan saboda barzanar cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu