Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Shekara kenan ba a samu mamatan Korona a Afrika ta Kudu ba

A karon farko tun watan Maris na shekarar bara,  ba a samu mutun ko guda da cutar Korona ta kashe a Afrika ta Kudu ba kamar yadda hukumomin kiwon lafiyar kasar suka bayyana.

Wasu majinyatar Korona
Wasu majinyatar Korona AP - Kin Cheung
Talla

Annobar ta Korona ta yi wa Afrika ta Kudu mummunar illa fiye da kowacce kasa a nahiyar Afrika, inda kusan mutane dubu 100 suka mutu a kasar bayan kamuwa da cutar ta Korona.

Yanzu haka dai an lura da cewa, daukacin asibitocin kasar babu wadda ke dauke da marar lafiyar cutar ta Corona kamar yadda Shabir Madhi kwarare ta fannin allurar rigakafi a jami’ar Witwatersrand ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP

Ya kuma kara da cewa, sun sani an samu asarar rayuka da dama, amma kuma  wannan ya bai wa mafi yawan al’ummar kasar damar daukar matakan kariya kan munanan nau’ukan cutar na covid 19 da suka bulla a kasar

Akalla kashi  80% na babban yankin Gauteng da ke dauke da cinkoson jama’a, inda birnin Johannesburg ya ke, da tuni ya harbu da cutar ta Covid, inda aka samu mafi yawan yaduwar cutar da ya kai kusan na daukacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.