Isa ga babban shafi

Tafiyar mintuna biyar dauke da jariri na sassauta kukansa - Masana

Masana kimiyya sun fitar da wani rahoton bincike da ke bayyana yadda za a shawo kan jariran da ke tsananin kuka.

Masana sun ce tafiya da jariri ana jijjiga shi tsawon minti biyar na hanashi kuka tare da sanya shi barci nan take
Masana sun ce tafiya da jariri ana jijjiga shi tsawon minti biyar na hanashi kuka tare da sanya shi barci nan take Getty Images - FatCamera
Talla

Dabarun kwantar da hankalin jariran an samo su ne daga gwaje-gwajen da aka yi a Japan da Italiya, wadanda aka yi nazari kuma aka buga su a mujallar Current Biology.

Masu binciken sun ce suna fatan binciken zai iya amfanar da iyaye da suke cikin damuwa, musamman ma wadanda ba su da kwarewa wajen kula da kananan yara.

A baya dai tawagar ta yi nazari kan dabbobi masu shayarwa da ke haihuwa da ba su iya kula da kansu, kamar su beraye, karnuka, birai da sauransu.

Binciken ya gano cewa, lokacin da wadannan dabbobin suka dauki jariransu suka fara tafiya, yaran suna yin shiru kuma suna natsuwa, kuma bugun zuciyarsu na sauka a hankali.

Dakta Kuroda da abokan aikinta sun so su kara bincika wannan a cikin mutane, kuma su kwatanta tasirin da wasu halaye masu kwantar da zuciya kamar girgiza jariri a wuri guda.

Tawagar masu binciken, sun dauki nau'i-nau'i har guda 21 na iyayen yara daga farkon haihuwa zuwa watanni bakwai, kuma sun gwada su a karkashin sharudda hudu: daukar jariran lokacin da suke motsi, wasu jariran iyayen su za su dauke su lokacin da suke zaune, wasu kuma lokacin da suke kwance, ko kuma wadanda aka ajiye su a cikin bargo.

Kukan jariran ya kai ragu kuma bugun zuciyarsu na raguwa a cikin dakika 30 lokacin da ake tafiya da su. Akwai irin wannan tasirin lokacin da ake dan jijjiga su, amma hakan baya tasiri a lokacin da ake rike da su kawai ba.

Wannan ya ba da shawarar cewa, sabanin zato, lallabawa kamar jariri yana mahaifa bai isa ya lallaba shi a duk lokacin da yake kuka, amma daukar sa ko da a kafada ko kuma a rungume ana tafiya, shi ke saurin sassauta zuciyar yaro.

Bayan haka, sun duba tasirin daukar jarirai na tsawon dakika biyar, inda suka gano cewa hakan ya sa kashi 46 cikin 100 na sanya su yin barci, kuma karin kashi 18 cikin dari su na yin barci a cikin dakikoki kadan.

Wannan ya nuna cewa, ba wai daukar jaririn ana tattaki da shin a hana shi yin kukan kadai ba, a wasu lokutan hakan na sanya su yin bacci cikin salama.

Amma akwai karin bayani da ke nuna cewa, lokacin da aka kwantar da jarirai, fiye da kashi daya cikin uku suna fahimtar hakan cikin dakika 20.

Gwajin na’ura ya nuna cewa bugun zuciyar jariran na tashi daga lokacin da aka janye su daga jikin mahaifiyarsu.

Duk da haka, lokacin da jariran suka yi barci na tsawon lokaci kafin a kwantar da su, suna daukar dogon lokaci kafin su farka.

Kuroda ta ce wannan abin mamaki ne matuka, domin ta dauka wasu abubuwa kamar yadda aka kwantar da su a gado ko kuma yanayinsu zai taka rawa, amma ba haka lamarin yake ba.

Ta ce "hankalinmu yana da iyaka, shi ya sa muke bukatar kimiyya."

Dangane da jimillar binciken da suka yi, sun ba da shawarar wata ka'ida don kwantar da hankali da inganta barcin yaro, a rika yin tattaki kamar na tsawon dakika biyar dauke da jariran, sannan a zauna rike da su shim ana tsawon dakika kamar biyar zuwa takwas, kafin a sa su yin barcin.

Tawagar masu binciken ta ce shakka babu wannan, na saurin kwantar da hankulan jarirai, sabanin sauran hanyoyin kamar barin jariri ya yi kuka da kansa ya yi barci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.