Isa ga babban shafi

Cutar korona na ci gaba da kasancewa barazana a Afirka - CDC

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afirka, ta ce cutar ta Covid-19 har yanzu barazana ce ga nahiyar,  idan aka yi la'akari da karancin allurar rigakafin cutar a kasashen yankin.

Allurar rigakafin cutar korona kena
Allurar rigakafin cutar korona kena © iStock /kovop58
Talla

Da yake magana yayin wani taron manema labarai a shugaban hukumar, Ahmed Ogwell Ouma ya ce sama da kashi 22% na al'ummar Afirka ne ke da cikakkiyar allurar riga-kafi wanda ke nufin har yanzu cutar tana ci gaba da zama a Nahiyar.

Kalaman na sa sun ci karo da kalaman shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus da ke cewa a yanzu haka ana gab da kawo karshen cutar ta COVID.

Hukumar ta CDC ta ce za ta ci gaba da mai da hankali wajen ganin an yi wa mutane da dama allurar riga-kafi.

Kasashen Afirka sun yi gwagwarmaya don samar da kayayyakin rigakafin COVID yayin da kasashe masu arziki ke ci gaba da inganta hanyoyin samarwa al’ummomin su rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.