Isa ga babban shafi

Uganda ta tabbatar da bullar cutar Ebola bayan mutuwar wani mutum

Uganda ta tabbatar da bullar cutar Ebola a tsakiyar gundumar Mubende ta kasar bayan mutuwar wani mara lafiya mai shekaru 24.

Cutar Ebola dai na saurin yaduwa da kuma kisa
Cutar Ebola dai na saurin yaduwa da kuma kisa © Finbarr O’Reilly pour la Fondation Carmignac
Talla

Rahotanni na cewa mutumin mazaunin gundumar Mubende, mai tazarar kilomita 150 yamma da Kampala babban birnin kasar.

Da yake magana da manema labarai, babban sakataren ma'aikatar lafiya ta Uganda, Dakta Atwine ya ce "Lokacin da aka kai rahoto zuwa asibiti, mutumin ya nuna alamun da ake zargi da cutar Ebola, abinda ya sa aka kebe shi tare da gudanar da gwaje-gwaje a kan sa.

Har yanzu dai ba a san yadda aka yi ya kamu da cutar ba amma tun farko an yi masa gwajin wasu cututtuka da suka hada da zazzabin cizon sauro a lokacin da ya nemi kulawa a kauyensu.

Sama da shekaru goma ke nan rabon da Uganda ta fitar da rahoton wanda yak amu da cutar mai saurin yaduwa, in ji WHO.

Tabbatar da hakan ya biyo bayan wani bincike da cibiyar  bada agajin gaggawa ta gudanar bayan zargin mutuwar mutane da dama a gundumar a wannan watan.

A cewar WHO, yanzu haka mutane takwas da ake zargi na dauke da cutar a halin yanzu suna samun kulawa a wata cibiyar lafiya.

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da ke makwabtaka da Uganda sun ce a cikin watan Agusta, an samu bullar wata sabuwar cutar da ake dangatawa da Ebola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.