Isa ga babban shafi

Ana bukatar dala biliyan 18 don yaki da tarin fuka, zazzabin cizon sauro da HIV

Asusun Yaki da Cuta mai karya garkuwa jiki, tarin fuka da zazzabin cizon sauro ya nemi tara akalla dala biliyan 18 a wani taron bayar da agaji da shugaban Amurka Joe Biden ya jagoranta, yayin da shekaru da dama da aka shafe ana da yaki da cututtukan, annobar Covid19 ta mayar da shi baya.

Samantha Power
Samantha Power © rfi
Talla

Wannan dai shi ne burin ci gaba mafi girma da asusun ya gindaya, wanda ya hada gwamnatoci, hukumomi, kungiyoyin farar hula da kamfanoni masu zaman kansu.

Ci baya ba makoma bane, in ji shugabar Hukumar ta USAID Samantha Power. "Muna da ilimi, kayan aiki, akwai tsarin da ya dace don sake dawowa da kuma ci gaba da yunkurinmu na kawo karshen wadannan cututtuka."

Akwai abubuwa da yawa masu hadari da ke tafe, kuma shirin dala biliyan 18 ya dogara sosai kan kawo karshen cutar sida, tarin fuka da zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030, sake farfado da wuraren da aka rasa sakamakon barkewar cutar Covid, tare da ceton rayukan da bai gaza miliyan 20 ba a cikin shekaru uku masu zuwa sune mafarkinmu," in ji Samantha.

Adadin ya zarce kashi 30 cikin 100 fiye da wanda aka samu a karo na shida kuma na baya bayan nan, wanda shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya karbi bakunci a shekarar 2019, inda a wancan lokaci aka tara dala biliyan 14.

A shekarar da ta gabata, Asusun na Duniya ya yi gargadin cewa barkewar cutar Coronavirus na yin “mummunan tasiri” kan aikinta, wanda ya haifar da raguwar sakamako a karon farko a tarihin shirin.

Sai dai asusun na duniya, wanda ke bayar da kashi 76 cikin 100 na duk wani tallafi ga duniya don yaki da cutar tarin fuka, ya ce shirye-shiryen tunkarar kalubalen sun nuna alamun farfadowa a bara.

Hakazalika, adadin mutanen da aka aka samu na masu kamuwa da cutar HIV ya sake karuwa bayan raguwar da aka samu a cikin 2020, inda ya kai miliyan 12.5 a duniya.

Rushewar ayyukan kiwon lafiya a lokacin bala'in Covid, ya haifar da asarar rayuka a yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro, wanda ya yi sanadiyar mutuwar kashi 12 cikin 100 a shekarar 2020, zuwa kimanin 627,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.