Isa ga babban shafi

Dole a hukunta kamfanin da ya yi sanadin mutuwar yara 70 - Gambia

Majalisar dokokin kasar Gambia ta ba da shawarar a haramta amfani da magani mallakar wani kamfanin harhada magunguna na kasar Indiya tare da neman a gurfanar da shi gaban kuliya kan mutuwar akalla yara 70 sakamakon kamuwa da ciwon koda.

Kwamitin ya ce ana ci gaba da gudanar da binciken kimiyya a kan musabbabin mutuwar yaran da suka samu munanan ciwukan koda.
Kwamitin ya ce ana ci gaba da gudanar da binciken kimiyya a kan musabbabin mutuwar yaran da suka samu munanan ciwukan koda. AFP - MILAN BERCKMANS
Talla

"Ya kamata gwamnati ta bi doka a kan Maiden Pharmaceuticals saboda fitar da gurbatattun kwayoyi zuwa Gambia," in ji rahoton kwamitin da aka kafa a watan Oktoba.

Hukumar Lafiya ta Duniya a watan Oktoba ta ba da sanarwa game da maganin tari guda hudu da Maiden Pharmaceuticals da ke arewacin Indiy ke sarrafawa.

Gwajin dakunan gwaje-gwaje ya gano matakan da kamfanin ya bi wajen sarrafa magungunan,  wanda hakan barazana ce babba ga rayuwar yara, in ji WHO, tare da cewa mai yiwuwa an rarraba magungunan a wasu kasashen bayan Gambia da ke yammacin Afirka.

Kwamitin majalisar dokokin Gambiya ya ba da shawarar a ranar Talata cewa hukumar kula da magunguna ta kasar (MCA) ta  jefa sunan kamfanin cikin bakin littafi da kuma haramta amfani da duk wani magani da kamfanin ke sarrafawa tare da sayarwa a kasuwannin Gambia.

Kwamitin ya ce ana ci gaba da gudanar da binciken kimiyya a kan musabbabin mutuwar yaran da suka samu munanan ciwukan koda.

Amma duk da haka, kwamitin ya ce yana da yakinin cewa "Maiden Pharmaceuticals Ltd. na da laifi kuma ya kamata a dora masa alhakin fitar da gurbatattun magungunan da ke da alaka da mutuwar akalla yara 70 a Gambia.

Tuni dai gwamnatin Gambia ta yi gargadin kan amfani duk wani maganin tari da ke yaduwa a cikin kasar da kuma duk wani nau'in magunguna da kamfanin Maiden Pharmaceuticals ke sarrafawa, wanda aka rufe masana'antar sarrafa su da ke Indiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.