Isa ga babban shafi

Girman matsalar dumamar yanayi ta zarce rahoton masana da rubanye 3- Kwararru

Wani gagarumin aikin sa ido ta hanyar amfani da taurarin dan adam da kwararru suka kaddamar a ranar Laraba, ya bayyana cewa, girman matsalar dumamar yanayi sakamakon iska mai gubar da kamfanoni masu amfani da fetur ko Iskar gas ke fitarwa, ya ninka sau uku, fiye da yadda rahotanni ke bayyanawa.

Kwararru sun bayyana gano wurare fiye da dubu 70,000 da ke bulbular da iska mai guba cikin iskar da ke kewaye da duniyar da muke, wadda aka fi sani da Atmosphere a turance.
Kwararru sun bayyana gano wurare fiye da dubu 70,000 da ke bulbular da iska mai guba cikin iskar da ke kewaye da duniyar da muke, wadda aka fi sani da Atmosphere a turance. AP - Manish Swarup
Talla

Bayanan farko da taurarin dan adam din da aka kaddamar da fara ayyukansu yayin taron duniya kan sauyin yanayi na COP27 a Masar, sun bayyana gano wurare fiye da dubu 70,000 da ke bulbular da iska mai guba cikin iskar da ke kewaye da duniyar da muke, wadda aka fi sani da Atmosphere a turance.

Wannan katafaren aiki da ‘Climate Trace’ wata gamayyar cibiyoyin bincike, da kungiyoyin agaji da kuma kamfanoni ke gudanarwa, yana sa ido ne akan wuraren da suka kunshi manyan masana'antu, kamfanonin samar da makamashi da na ayyukan gona, hakar ma’adanai, sarrafa shara da kuma sufurin ababen hawa.

Bayan tattara bayanai daga taurarin dan adam sama da 300, da kuma dubban na'urori masu kwakwalwa akan tudu da kuma cikin teku, kwararrun sun gano cewar kamfanoni 14 da ke kan gaba wajen fitar da gurtaciyyar iska, dukkaninsu na gudanar da ayyukan tono albarkatun man fetur ne da iskar gas.

Daga cikin cikin manyan kamfanonin kuma, Permian Basin da ke jihar Texas a Amurka ne da ya mallaki filayen hakar mai da iskar gasa mafi girma a duniya, ya fi kowane kamfani bulbular da iska mai gubar da ke ta’azzara dumamar yanayi a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.