Isa ga babban shafi
Najeriya

Sharhi akan Jam’iyyar PDP da ‘yan Takararta

Jam’iyyar PDP Jam’iyya ce wacce ta kwashe shekaru 10 tana mulkin Nigeria tun a zaben shekarar 1999 bayan da sojoji suka mika mulki ga farar hula. Kuma har yanzu jam’iyyar ce ke mulkin kasar tare da samun rinjayen kujerun ‘yan majalisu da gwamnnonin jahohi.A zaben shekarar 1999 Cip Olusegun Obasanjo ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar, wanda ya yi tazarce a zaben shekarar 2003. Marigayi Ummaru Musa Yar’Adua ne kuma ya lashe zaben shekarar 2007 karkashin tutar jam’iyyar inda daga bisani bayan rasuwarsa mataimakinsa Goodluck Ebele Jonathan aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, wanda a yanzu haka ke takara karkashin jam’iyyar a zaben 2011.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan da Namadi Sambo
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan da Namadi Sambo
Talla

Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan

Sai dai kuma ana danganta nasarorin da jam’iyyar ke samu na lashe zabe a kasar da tabka magudi da arin-gizon kuri’u.

Tun farkon kafa jam’iyyar a Najeriya, manyan jiga-jigan jam’iyyar suka amince da tsarin mulkin karba-karba tsakanin sassan yankunan kasar musamman yankin Arewaci da kudanci, al’amarin da ya sanya shiyar arewa suka amince da Obasanjo daga yankin kudanci a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 1999 da 2003. Sai a zaben shekarar 2007 jam’iyyar ta tsayar da Ummaru Musa Yar’adua daga yankin Arewaci a matsayin dantakara, amma bayan rasuwarsa aka samu sabani tsakanin ‘yayan jam’iyyar musamman wajen tsayar da dantakara a zaben shekarar 2011.

Wasu daga yankin arewaci suna ganin Goodluck Jonathan bai kamata ya tsaya takara

Shugaba Goodluck Jonathan Ya Kaddamar Da Yakin neman zabe na Lagos

ba domin lokacin mulkin arewa ne amma shugaban ya yi watsi da tsarin jam’iyyar inda ya kafa madogarar kundin tsarin mulkin wanda ya bashi damar tsayawa takara.

Bayan gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar wanda shugaban ya lashe tsakaninsa da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da Sarah Jibril, a yanzu haka shugaban da shi da matakinsa Namadi Sambo ne zasu tunkari zaben shugaban kasa a watan Aprilun bana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.