Isa ga babban shafi
Nigeria

Direbobin motocin dakon kaya a Lagos sun yanke shawarar shiga yajin aikin sai baba ta gani daga gobe talata

Kungiyar direbobin motocin dakon kaya ta jahar Lagos a tarayyar Nigeriya, ta bayyana tsunduma cikin yajin aikin har illa masha’a Allahu a gobe talata, dangane da korarsu da gwamnatin jahar ta yi, daga inda suke aje motocinsu ba tare da basu wani gurin ba. Ta bakin shugaban kungiyar Alhaji Usaini Umar Pateskum mahukumtan jahar ta Lagos sunci zarafinsu lokacin da suka tarwatsa su daga karkashin gadar Marin Beach, shima da kansa ya sha duka kafin a jefa shi a Balck Maria. dan haka a cewarsa wannan yajin aiki da zasu fara a gobe talata babu ja da baya har sai an basu wani sabon matsugunnin.suma masu saida kayan abinci dangin dabbobi da Kayan gwari sun bayyana goyan bayansu dangane da wannan yajin aiki  

(Photo : Lei Yang/DR)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.