Isa ga babban shafi
Nigeria

Wasu dalibai sun kone gidaje 12 a Patakwal

DALIBAN Jami’ar Patakwal dake yankin neja Delta a Nigeria, jiya sun gudanar da zanga zanga, inda suka kona gidaje 12 a garin Aluu, inda mutanen garin suka kona wasu dalibai hudu har lahira.Daliban da ma daukacin Yan Nigeria sun harzuka ne lokacin da aka yada hotunan takwarorin nasu ta yanar gizo, lokacin da aka musu tsirara, aka musu dukan kawo wuka, kana aka sanya tayar mota a wuyan kowanne daya daga cikin su, aka kona, saboda zargin satar wayar salula da na’urar computa.Rahotanni sun ce daliban jami’oi daga sassa dabam dabam na Yankin Kudu maso gabas da kudu maso kudu, sun shiga zanga zangar.Tuni dai jami’an tsaro suka kama mutane 13 ciki harda Sarkin garin, Chief Hassan Walewa, saboda kisan. 

Daliban da aka kashe a Jami'ar Patakwal
Daliban da aka kashe a Jami'ar Patakwal
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.