Bakonmu a Yau
Dakta Ibrahim Yakubu Lame Tsohon Ministan 'Yan sandan Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 02:58
Dattijan daga shiyyar Arewa maso Gabas a Najeriya, sun kammala wata tattaunawar share fage a garin Bauchi, game da babban taron kaddamar da wannan kungiyar da zata ceto wannan yankin Arewa da ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arziki. A Hirar shi da RFI Dakta Ibrahim Yakubu Lame kakakin kungiyar ya yi bayani akan yadda za su cim ma wannan buri, ganin cewa mambobin wannan kungiyar ba su cikin gwamnati.