Isa ga babban shafi
Nigeria

An sace mahaifiyar Ministan kudin Nigeriya

Wasu Yan bindiga sun sace mahaifiyar Ministan kudin Nigeriya, Ngozi Okonjo-Iweala, a garin su dake Ogwashi uku, a Jihar Delta.Bayanai sun ce, wasu mutane 10 ne suka sace mahaifiyar Ministan mai shekaru 82 ne a fadar Sarkin garin, Prof Chukwuka Okonjo da misalin karfi daya da rabi na rana.Mai magana da yawun Yan Sandan Jihar Delta, DCP Charles Muka, ya tabbatar da labarin, kuma ya zuwa yanzu dai, babu wanda ya dauki alhakin sace gyatumar. 

Ministan kudin Nigeria Ngozi Okonjo-Iweala
Ministan kudin Nigeria Ngozi Okonjo-Iweala REUTERS/Brendan McDermid
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.