Isa ga babban shafi
Nijeriya

Kungiyar EU da MDD za su samar da ruwan sha a Neja Delta

Kungiyar Kasashen Turai da Asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya sun sanya hannu akan wata yarjejeniyar shekaru biyar, da zata bada damar da samar da tsabtacacen ruwan sha, ga al’ummomin Jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo da Rivers a Nijeriya.Kungiyar tace, aikin na daga cikin shirin kwantar da hankalin al’ummomin Niger Delta, mai fama da tashin hankali.Matasan yankin na Neja Delta sun dade suna tayar da kayar baya, kan zargin da suke yi na amfani da dumbin arzikin da yankin nasu ke da shi wajen jin dadin wasu tsiraru a kasar, a yayin da su kuma ake barin nasu ba tare da ababen more rayuwa ba.  

Irin matsalolin ruwan sha da wasu sassan nahiyar Afrika ke fama da shi
Irin matsalolin ruwan sha da wasu sassan nahiyar Afrika ke fama da shi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.