Isa ga babban shafi
Brazil

Kasar Brazil na hankoron samun babban matsayi a harkar makamashin Najeriya

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta bayyana kudirin gwamnatin kasar Brazil na kara bunkasa dangantakar ta, da tarayyar Najeriya wajen samar da makamashin wutar Lantarki da Kwal, da Iskar Gas da dai sauran sassan samar da makashi daban-daban

Na'urorin sarrafa makamashi a tarayyar Najeriya
Na'urorin sarrafa makamashi a tarayyar Najeriya
Talla

Dilma Rousseff ta bayyana kudurin kasar Brazil ne kan batun samar da ingantaccen makamashin hasken Wutar Lantarki a tarayyar Najeriya mai dimbin albarkatun Man Fetir, bayan kammala taro da shugaba Goodluck Jonathan.

Najeriya dai ta kasance babbar abokiyar kawancen kasar Brazil ta fanning kasuwanci, yanzu haka kasashen biyu sun kulle wata yarjejeniya ta kasuwancin data kai Dollar Amurka Billiyan daya da rabi, kwatankwacin Euro Billiyan daya da Miliyan dari daya a shekarar 2002, yawan kudin daya kai Dollar Billiyan 9 a shekarar data gabata.

Kamfanin mai na Petrobras mallakar kasar Brazil ma, ya saka hannayen jari na akalla daruruwan miliyoyin Dololi a wajen harkar makamashin Kwal, da Man Fetir, da Iskar Gas da sauran sassan da ake samun makamashi a tarayyar Najeriya.

Dilma Rousseff hakama ta bayyana cewar kasar Brazil na shirin kara fadada huldarta da tarayyar Najeriya ta fannin samar da hasken Wutar Lantarki ta cikin Koguna da sauran su.

Kwararru na ganin cewar kasar Brazil a ‘yan kwanakin nan ta kara mika Hannayen ta zuwa kasashe masu arziki irin su tarayyar Najeriya ne, domin ta samu hanyar tabbatar da cigaban da take samu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.