Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana ci gaba da Allah wadai da kalama Asari Dokubo

Masu fada a ji a Nigeria suna ci gaba da Allah wadai da kalaman da tsohon mai tayar da kayar baya a yankin Neja-Delta, mujahid Asri Dokubo ya yi, kan barazanar yaki a kasar, in har ba a zabi Shugaba Goodluck jonathan ba, a matsayin shugaban kasar a shekarar 2015. GWAMNONIN Arewacin Nigeria da Majalisar wakilan kasar sun bukaci kama Asari Dokubo, kan barazanar jefa kasar cikin tashin hankalin da yayi.Shugaban Gwamnonin, Dr Babangida Aliyu, ya bayyana kalaman a matsayin barazana ga zaman lafiyar kasa, yayin da Majalisar wakilai tace kalaman nasa na iya jefa Nigeria cikin rudani.Shi kuwa tsohon minista, Chief Edwin Clark, gargadi yayi kan masu barazanar tashin hankali idan Jonathan bai yi nasarar zabe ba, inda yake cewa ‘Yan Nigeria ne zasu iya mayar da shi karaga, ba ’yan kabilar Ijaw, ko kuma mutanen kudu maso kudu ba. 

Asari Dokubo
Asari Dokubo myondostate.com
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.