Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Akwai sauran rina a kaba game da kudadenmu na lada - Enyeama

A yayin da Najeriya ke shirin karawa a yau a wasan ta na farko, mai tsaron ragar kasar, kuma kaftin din ‘yan wasan na Najeriya, Vincent Enyeama, ya ce har yanzu takaddama ba ta kare ba game da kudadensu da suk nema a biya sun a lada.

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya
'Yan wasan Super Eagles na Najeriya Reuters
Talla

Sai dai ya ce ‘yan wasan za su ajiye batun a gefe a yanzu, domin kada Najeriyan ta yi kasa a gwiwa a yayin da za ta fara kara a yau da kasar Tahiti.

Takaddamar rashin biyan kudaden na ‘yan wasan ya sa Najeriya ba ta isa kasar Brazil akan lokaci ba sai a daren shekaran jiya Asabar.

A yanzu haka Brazil ce ke saman teburin rukunin "A" da maki uku, inda take biye da Italiya da maki uku a yayin da a rukunin B kuwa Spain ke sama da maki uku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.