Isa ga babban shafi
Faransa

Ministan Faransa ya zargi kungiyar kasashen Turai da hura wutar rikicin siyasar kasar

Wani Ministan kasar Faransa ya zargi kungiyar Tarayyar Turai da hura wutar rikicin siyasar kasar tsakanin Gwamnatin Jam’iyyar Gurguzu mai mulki da kuma ‘yayan Jam’iyya masu tsananin kishin kasa.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande Reuters / Platiau
Talla

Wannan zargin dai ya fito ne daga bakin Ministan masana’antu Arnaud Montebourg, wanda ya ce shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso shi ke karawa ‘yan kishin kasa samun kwarin giwar ci gaba da adawa da gwamnati.

Wannan kuma ya shafi kalaman da Borroso ya yi ne a game da matakin Faransa na kin amincewa da matakin janye bangaren masana’antar fina finai da Talabijin a cikin yarjejeniyar kasuwannin duniya.

Ministan na Faransa ya ce hakan ke fito da matsalolin shugabannin Kungiyar Turai saboda karfin da aka basu.

Kuma a cewar shi wannan ne ya budewa ‘yan kishin kasa samun damar sukar gwamnatin da al’umma suka zaba.

Akwai dai yarjejeniya da kungiyar kasashen Turai ke kokarin kullawa da Amurka, kuma Faransa ce ta jagoranci taron ministocin harakokin kasuwancin game da bukatun yarjejeniyar da za su cim ma.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.