Isa ga babban shafi
Nigeria

Jama'iyyar APC a Najeriya ta nemi 'yan majalisarta su yi wa gwamnatin kasar bore

Jam’iyyar APC mai adawa a Nigeria, ta bukaci ‘yayanta a cikin zauren majalisar wakilan kasar da kada su amince da duk wani kuduri da zai fito daga gwamnatin kasar cikinsu kuwa har da kasafin kudin kasa da kuma nada sabbin shugabannin sojoji na kasar, har zuwa lokacin da gwamnatin za ta kawo karshen abinda jam’iyyar ta kira kama karya da jami’an tsaro ke yi a jihar Rivers.Jam’iyyar ta APC ta dauki wannan mataki ne a taron da shugabanninta na kasa suka gudanar da ya samu halartar gwamnonin jama’iyyar su 16.A wani bangaren kuma, yayin da ‘yan majalisun dokokin Nigeria ke ci gaba da canza sheka zuwa wasu jama’iyyun, lamarin da ya ci gaba da haifar da cececkuce a fagen siyasar kasa, tuni aka fara samu rudani kan lamarin.Dan Majalisar Wakilan kasar, mai wakiltar mazabasr Jos ta Arewa da Bassa, Hon. Suleiman Kwande, ya nesanta kanshi daga wasikar da ja’iyyar shi ta aike wa majalisar cewa ya koma jama’iyyar PDP.Hon. Kwande yace jama’ar mazabar shi suna fatan ganin ya koma APC, don haka ya yanke shawarar komawa inda al’ummar tashi suke son ganin ya koma. 

Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal
Kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal nigeriansabroadlive.com
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.