Nigeria
Shugabannin Yarabawa Na Kaunar Taron Kasa
Shugabannin alummar Yarabawa dake kudu maso yammacin Nigeria sun bayyana amincewar su ga taron kasa da Gwamnati ke shirin yi, inda suka tsaida shawarar ganin an baiwa Gwamnatocin shiyyoyin kasar ‘yancin kai sosai da sarrafa arzikin da Allah ya hore masu ba tare da katsalandan daga Gwamnatin tarayya ba.Jiga-Jigan alummar yarabawan sun fadi cikin wata sanarwa bayan taro a garin Ishara-Remo dake jihar Ogun cewa zasu ga lallai ilahirin yarabawa sun fito da murya guda alokacin babban taron kasar dake tafe.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: