Isa ga babban shafi
Najeriya

Ana zanga a Kano saboda zargin sake jirgin saman da aka kama dauke da makamai

Wasu matasan birnin Kano, suna can suna zanga zangar neman ganin an yi bincike kan jirgin saman kasar Rasha, da aka kama dauke da makamai a filin jirgin saman na Malam Aminu Kano. Zuwa wannan lokacin wakilinmu dake birnin ya sanar damu cewa jami'an 'yan sanda, dana rundunar tsaro ta SS suna can suna kokarin tarwatsa matasan.sai dai babu rahoton wata hatsaniya sakamakon zanga zangar, da gamayyar wasu kungiyoyin fafaren hula suka shirya.Rahotanni masu karo da juna suna ci gaba da fitowa daga kasar ta Nigeria, kan ci gaba da rike, ko sakin jirgin da aka kama din.A baya dai ofishin jakdancin kasar Rasha a Nigeria ya nesanta kasar da Jirgin, sai dai kuma daga baya ya amincea da cewa na kasar ne, amma yana duke ne da kayan yakin kasar Faransa.Shima jakadan Faransa a Nigeria Jacques Champagne de Labriolle, yace jirgin na dauke ne da kayan aikin sojan da aka kwashe daga kasar Jamhuriyar Africa ta Tsakiya. 

Matasan dake zanga zanga a birnin Kano na Nigeria
Matasan dake zanga zanga a birnin Kano na Nigeria RFI/Dandago
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.