Isa ga babban shafi
Nigeria

Motar ‘yan Buki da Tankar yaki sun yi taho-mu-gama a Najeriya

Mutum 7 ne suka mutu a yayin da wasu 18 suka samu munanan Raunuka a wani hatsarin Motar Bus dauke da ‘yan bukin Aure ta fadawa wata tankar yaki ta Sojin Najeriya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya

Zaidi ya watu 40 wamefariki katika ajali iliyotokea katika mkoa wa Iringa, Tanzania.
Zaidi ya watu 40 wamefariki katika ajali iliyotokea katika mkoa wa Iringa, Tanzania. RFI-KISWAHILI
Talla

Hatsarin dai ya auku ne da yammacin Jumu’a lokacin da Motar Bus din da ke makare da Mata da kananan Yara masu dawowa daga wani bukin Aure ta yi taho mu gama da tankar yaki ta Sojin Najeriya a garin Azare na jihar Bauchi.

Direban motar bus din dai ya kasa shawo kanta ne, bayan da Tayar gaba ta fashe jim kadan da fita garin Azare, sannan suka caba da motar Tankar yakin da ke zuwa daga dayan bangaren hanyar.

Dukkanin wadanda suka mutu dai daga ita Motar Bus din suke, babu ko daya daga bangaren Dakarun Gwamnati da ke a cikin Tankar da ya mutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.