Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya ciyo bashi don raya yankin da ke fama da Boko Haram

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ciyo bashin sama da Dala bilyan biyu domin raya yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da ayyukan kungiyar Boko Haram. Shugaban kasar Muhammadu Buhari ne ya fadi haka a birnin Washington na Amurka.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari AFP via telegraph
Talla

Shugaban Buhari wanda yanzu haka ke ziyarar aiki a kasar Amurka a jawabinsa jim kadan bayan ya gana da jami’an bankin na duniya a birnin Washington, ya ce yankin na arewa maso gabashin Najeriya ya tagayyara ainun, kuma yana bukatar a sake gina shi.

Shugaban da ya karbi mulki kusan wattani biyu da suka shude inda ya yi alkawarin warware matsalolin kasar da suka shafi tashe-tashen hankula sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram da ya hallaka mutane sama da dubu goma tare da tilastawa miliyoyi tserewa daga gidajensu.

Buhari kuma ya ce matakin wata dama ce ta kula da rayuwar duban mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.

Babu dai ruwa a Bashin da Najeriya ta karba daga nan har zuwa shekaru 10 na farko.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.