Sojin Najeriya sun lalata sansanonin Boko Haram
Rundunar sojin Najeriya ta lalata sansanonin biyar da mayakan Boko Haram ke amfani da su a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin Najeriya ya fitar, Kanal Sani Usman ta bayyana cewa, sojoji sun lalalata sansanonin mayakan da ke Hausari da Baranga a karamar hukumar Marte.
Sanarwar ta ce, sojin sun kaddamar da wannan farmakin ne a wani mataki na ci gaba da kokarin kwato wuraren da Boko Haram ta karbe tare da kawo karshen kungiyar.
Sojin Najeriya sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram biyu a fafatawar da suka yi da juna a sansanonin, baya ga makaman da suka karbe na mayakan kamar yadda sanarwa ta bayyana.
Har ila yau sanarwar ta ce, a watan jiya ne runduna ta 5 ta lalata sansanonin Boko Haram guda 20 a yankin Kerenowa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu