Isa ga babban shafi
Najeriya-kano

Mutane da dama ake zaton harin bam a Kano ya ritsa dasu

Rahotanni daga Jihar Kano arewacin Najeriya sun ce, an kai harin tawagen bama-bamai kan kasuwar wayoyin hannu dake unguwar Farm center. Harin da ke zuwa kwana guda bayan harin Yola daya kashe mutane sama da 30.

Wani harin bam da kungiyar Boko Haram ta taba kaiwa Kano
Wani harin bam da kungiyar Boko Haram ta taba kaiwa Kano REUTERS/Stringer
Talla

Wasu masu sana’a a kasuwar Nafiu Muhammed da Suleiman Haruna sun shaidawa Kamfanin dilanci labaran Faransa AFP cewa fashewar bama-bamai sun auku ne bayan La’asar, kuma masu aikin ceto sun isa wurin kan lokaci.

Tuni dai Jami’an tsaro suka isa idan harin ya auku, yayin da ‘yan kasuwan ke tserewa rayukansu.

Kawo yanzu dai ba a tantace adadin mamata ba sai dai ance mutane da dama ne suka jikkata.

Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na yawiata fusakantar hare-hare kungiyar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.